Back to Languages

Hausa - Chapter 10 - Yunus

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 15 — Surah Yunus 10:15

Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi.*" Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma