Back to Languages

Hausa - Chapter 10 - Yunus

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 2 — Surah Yunus 10:2

Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wan nan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne