Back to Languages

Hausa - Chapter 11 - Hud

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 61 — Surah Hud 11:61

Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa