Back to Languages

Hausa - Chapter 12 - Yusuf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 21 — Surah Yusuf 12:21

Kuma wanda ya saye shi daga Masar* ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba