Back to Languages

Hausa - Chapter 12 - Yusuf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 31 — Surah Yusuf 12:31

Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja