Back to Languages

Hausa - Chapter 12 - Yusuf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 40 — Surah Yusuf 12:40

Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba