Back to Languages

Hausa - Chapter 12 - Yusuf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 6 — Surah Yusuf 12:6

Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima