Back to Languages

Hausa - Chapter 13 - Ar-Rad

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 14 — Surah Ar-Rad 13:14

Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama* ba fãce yanã a cikin ɓata