Back to Languages

Hausa - Chapter 13 - Ar-Rad

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 41 — Surah Ar-Rad 13:41

Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako