Back to Languages

Hausa - Chapter 3 - Al-Imran

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 179 — Surah Al-Imran 3:179

Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai* Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba.** Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa.*** Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma