Back to Languages

Hausa - Chapter 3 - Al-Imran

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 186 — Surah Al-Imran 3:186

Lalle ne zã a jarraba* ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra