Back to Languages

Hausa - Chapter 30 - Ar-Rum

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 28 — Surah Ar-Rum 30:28

Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltuwa