Back to Languages

Hausa - Chapter 30 - Ar-Rum

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 48 — Surah Ar-Rum 30:48

Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi