Back to Languages

Hausa - Chapter 33 - Al-Ahzab

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Ahzab 33:1

Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima

Verse 2 — Surah Al-Ahzab 33:2

Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa

Verse 3 — Surah Al-Ahzab 33:3

Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli

Verse 4 — Surah Al-Ahzab 33:4

Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai

Verse 5 — Surah Al-Ahzab 33:5

Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai

Verse 6 — Surah Al-Ahzab 33:6

Annabi ne mafi cancanta* ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce

Verse 7 — Surah Al-Ahzab 33:7

Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su

Verse 8 — Surah Al-Ahzab 33:8

Dõmin Ya tambayi mãsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yã yi tattalin wata azãba mai raɗaɗi ga kãfirai

Verse 9 — Surah Al-Ahzab 33:9

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa

Verse 10 — Surah Al-Ahzab 33:10

A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah

Verse 11 — Surah Al-Ahzab 33:11

A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani

Verse 12 — Surah Al-Ahzab 33:12

Kuma a lõkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukãtansu ke cẽwa, Allah da Manzon Sa, "Ba su yi mana wa'adin kõme ba, fãce rũɗi

Verse 13 — Surah Al-Ahzab 33:13

Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutãnen Yasriba!* Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa, "Lalle gidãjenmu kuranye suke," alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu

Verse 14 — Surah Al-Ahzab 33:14

Kuma dã an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina (kãfirci), lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta (Madĩna) ba fãce kaɗan

Verse 15 — Surah Al-Ahzab 33:15

Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sunã yi wa Allah alkawari, a gabãnin wannan; Bã zã su jũya dõmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya

Verse 16 — Surah Al-Ahzab 33:16

Ka ce: "Gudun nan bã zai amfãne ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, bã zã a jĩshe ku dãɗĩ ba fãce kaɗan

Verse 17 — Surah Al-Ahzab 33:17

Ka ce: "Wãne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yã yi nufin wata cũta game da ku?" Kuma bã zã su sãmar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bã zã su sãmar wa kansu wani mataimaki ba

Verse 18 — Surah Al-Ahzab 33:18

Lalle Allah Ya san mãsu hana mutãne fita daga cikinku, da mãsu cẽwa ga 'yan'uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma bã zã su shiga yãƙi ba fãce kaɗan

Verse 19 — Surah Al-Ahzab 33:19

Suna mãsu rõwa gare ku, sa'an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda mutuwa. Sa'an nan idan tsõron ya tafi, sai su yi muku miyãgun maganganu da harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah

Verse 20 — Surah Al-Ahzab 33:20

Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan

Verse 21 — Surah Al-Ahzab 33:21

Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa

Verse 22 — Surah Al-Ahzab 33:22

Kuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da Manzon Sa suka yi mana wa'adi, Allah da Manzon Sa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa

Verse 23 — Surah Al-Ahzab 33:23

Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa,* kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa

Verse 24 — Surah Al-Ahzab 33:24

Dõmin Allah Ya sãka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai

Verse 25 — Surah Al-Ahzab 33:25

Kuma Allah Yã mayar *da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi

Verse 26 — Surah Al-Ahzab 33:26

Kuma Ya saukar *da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar

Verse 27 — Surah Al-Ahzab 33:27

Kuma Ya gãdar da ku gõnakinsu da gidãjensu da dũkiyõyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tãkarta bã. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kõme

Verse 28 — Surah Al-Ahzab 33:28

Yã kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kunã nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwãna kuma in sake ku, saki mai kyau

Verse 29 — Surah Al-Ahzab 33:29

Kuma idan kun kasance kunã nufin Allah da Manzonsa da gidan Lãhria, to, lalle, Allah Yã yi tattalin wani sakamako mai girma ga mãsu kyautatãwa daga gare ku

Verse 30 — Surah Al-Ahzab 33:30

Yã mãtan Annabi! Wadda ta zo da alfãsha bayyananna daga cikinku zã a ninka mata azãba ninki biyu. Kuma wancan yã kasance mai sauƙi ga Allah

Verse 31 — Surah Al-Ahzab 33:31

Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karamci

Verse 32 — Surah Al-Ahzab 33:32

Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri

Verse 33 — Surah Al-Ahzab 33:33

Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku,* kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã, ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa

Verse 34 — Surah Al-Ahzab 33:34

Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗãkunanku daga ãyõyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yã kasance Mai tausasãwa Mai labartawa

Verse 35 — Surah Al-Ahzab 33:35

Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma

Verse 36 — Surah Al-Ahzab 33:36

Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna

Verse 37 — Surah Al-Ahzab 33:37

Kuma a lõkacin* da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi,** kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa

Verse 38 — Surah Al-Ahzab 33:38

Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙã'idar, Allah a cikin (Annabãwa) waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce

Verse 39 — Surah Al-Ahzab 33:39

Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sunã tsõronSa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi

Verse 40 — Surah Al-Ahzab 33:40

Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme

Verse 41 — Surah Al-Ahzab 33:41

Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa

Verse 42 — Surah Al-Ahzab 33:42

Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice

Verse 43 — Surah Al-Ahzab 33:43

(Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikun Sa (sunã yi muku addu'a), dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai

Verse 44 — Surah Al-Ahzab 33:44

Gaisuwarsu a rãnar da suke haɗuwa da shi "Salãm", kuma Yã yi musu tattalin wani sakamako na karimci

Verse 45 — Surah Al-Ahzab 33:45

Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi

Verse 46 — Surah Al-Ahzab 33:46

Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa

Verse 47 — Surah Al-Ahzab 33:47

Kuma ka yi bushãra ga mũminai cẽwa, sũnã da falalamai girma daga Allah

Verse 48 — Surah Al-Ahzab 33:48

Kuma kada ka yi ɗã'a ga kãfirai da munãfukai, kuma ka ƙyãe cũtarsu (gare ka), kuma ka dõgara ga Allah. Allah Yã isa zama wakĩli

Verse 49 — Surah Al-Ahzab 33:49

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dãɗi* kuma ku sake su saki mai kyau

Verse 50 — Surah Al-Ahzab 33:50

Yã kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mãtanka waɗanda ka bai wa sadãkõkinsu da abin da hannun dãmanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bã ka na ganĩma, da 'yã'yan baffanka, da 'ya'yan goggonninka da 'yã'yan kãwunka da 'yã'yan innõninka waɗanda suka yi hijira tãre da kai, da wata mace mũmina idan ta bãyar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yanã nufin ya aure ta (hãlin wannan hukunci) kẽɓe yake gare ka, banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smũminai) game da mãtansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai

Verse 51 — Surah Al-Ahzab 33:51

Kanã iya jinkirtar da* wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri

Verse 52 — Surah Al-Ahzab 33:52

Waɗansu mãtã bã su halatta a gare ka a bãyan haka, kuma ba zã ka musanya su da mãtan aure ba, kuma kõ kyaunsu yã bã ka sha'awa, fãce dai abin da hannun dãmanka ya mallaka. Kuma Allah Yã kasance Mai tsaro ga dukan kõme

Verse 53 — Surah Al-Ahzab 33:53

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah

Verse 54 — Surah Al-Ahzab 33:54

Idan kun bayyana wani abu, kõ kuma kuka ɓõye shi, to, lalle Allah Ya kasance Masani ga kõme

Verse 55 — Surah Al-Ahzab 33:55

Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance Mahalarci a kan kõme

Verse 56 — Surah Al-Ahzab 33:56

Lalle, Allah da malã'ikun Sa sunã salati* ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi

Verse 57 — Surah Al-Ahzab 33:57

Lalle waɗanda ke cũtar Allah da Mauzon Sa Allah Yã la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãkantarwa

Verse 58 — Surah Al-Ahzab 33:58

Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dã muminai mãtã, bã da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne

Verse 59 — Surah Al-Ahzab 33:59

Yã kai Annabi! Ka* ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai

Verse 60 — Surah Al-Ahzab 33:60

Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu),* lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan

Verse 61 — Surah Al-Ahzab 33:61

Tsinannu ne duk inda suka shi za'a kame su kuma akarkashe su kashe

Verse 62 — Surah Al-Ahzab 33:62

A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shũɗe gabãninka, kuma bã zã ka sãmi musanyãwa ba ga hanyar Allah

Verse 63 — Surah Al-Ahzab 33:63

Sunã tambayar ka* ga Sã'a. Ka ce: "Saninta yanã wurin Allah kawai." Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa

Verse 64 — Surah Al-Ahzab 33:64

Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna

Verse 65 — Surah Al-Ahzab 33:65

Sunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki

Verse 66 — Surah Al-Ahzab 33:66

Rãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, "Kaitonmu, sabõda, rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo

Verse 67 — Surah Al-Ahzab 33:67

Kuma suka ce: "Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun* bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya

Verse 68 — Surah Al-Ahzab 33:68

Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma

Verse 69 — Surah Al-Ahzab 33:69

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci* Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah

Verse 70 — Surah Al-Ahzab 33:70

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya

Verse 71 — Surah Al-Ahzab 33:71

Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da Manzon Sa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma

Verse 72 — Surah Al-Ahzab 33:72

Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci

Verse 73 — Surah Al-Ahzab 33:73

Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai