Back to Languages

Hausa - Chapter 47 - Muhammad

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 2 — Surah Muhammad 47:2

Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu