Back to Languages

Hausa - Chapter 5 - Al-Maidah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 101 — Surah Al-Maidah 5:101

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin* da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri