Back to Languages

Hausa - Chapter 5 - Al-Maidah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 105 — Surah Al-Maidah 5:105

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci* rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa