Back to Languages

Hausa - Chapter 5 - Al-Maidah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 14 — Surah Al-Maidah 5:14

Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasãra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa