Back to Languages

Hausa - Chapter 5 - Al-Maidah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 15 — Surah Al-Maidah 5:15

Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, Manzon Mu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah