Back to Languages

Hausa - Chapter 5 - Al-Maidah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 94 — Surah Al-Maidah 5:94

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi