Back to Languages

Hausa - Chapter 59 - Al-Hashr

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Hashr 59:1

Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima

Verse 2 — Surah Al-Hashr 59:2

Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi,* daga gidãjẽnsu da kõra** ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri

Verse 3 — Surah Al-Hashr 59:3

Kuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã

Verse 4 — Surah Al-Hashr 59:4

Wannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne

Verse 5 — Surah Al-Hashr 59:5

Abin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai

Verse 6 — Surah Al-Hashr 59:6

Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga Manzon Sa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da Manzannin Sa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme

Verse 7 — Surah Al-Hashr 59:7

Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga Manzon Sa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na Manzon Sa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya* (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne

Verse 8 — Surah Al-Hashr 59:8

(Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da Manzon Sa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya

Verse 9 — Surah Al-Hashr 59:9

Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu,* sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo

Verse 10 — Surah Al-Hashr 59:10

Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai

Verse 11 — Surah Al-Hashr 59:11

Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci*ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne

Verse 12 — Surah Al-Hashr 59:12

Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba

Verse 13 — Surah Al-Hashr 59:13

Lalle kũ ne kuka fi bãyar da firgita a cikin zukãtansu bisa ga Allah, wannan kuwa dõmin sũ lalle waɗansu irin mutãne ne da bã su gãnẽwa

Verse 14 — Surah Al-Hashr 59:14

Bã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu irin mutane ne da bã su hankalta

Verse 15 — Surah Al-Hashr 59:15

Kamar misãlin waɗanda* ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai radaɗi

Verse 16 — Surah Al-Hashr 59:16

Kamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, "Ka kãfirta," To, a lõkacin da ya kãfirta ɗin, ya ce (masa): "Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron Allah Ubangijin halitta

Verse 17 — Surah Al-Hashr 59:17

Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. "Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci

Verse 18 — Surah Al-Hashr 59:18

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa

Verse 19 — Surah Al-Hashr 59:19

Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai

Verse 20 — Surah Al-Hashr 59:20

Yan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo

Verse 21 — Surah Al-Hashr 59:21

Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni

Verse 22 — Surah Al-Hashr 59:22

(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai

Verse 23 — Surah Al-Hashr 59:23

Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai tastãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi

Verse 24 — Surah Al-Hashr 59:24

Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa. Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima