Back to Languages

Hausa - Chapter 61 - As-Saf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 5 — Surah As-Saf 61:5

Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Alah ne zuwa gare ku?" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai