Back to Languages

Hausa - Chapter 66 - At-Tahrim

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah At-Tahrim 66:1

Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka,* kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai

Verse 2 — Surah At-Tahrim 66:2

Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware* rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima

Verse 3 — Surah At-Tahrim 66:3

Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini

Verse 4 — Surah At-Tahrim 66:4

Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne

Verse 5 — Surah At-Tahrim 66:5

Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta

Verse 6 — Surah At-Tahrim 66:6

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku* (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma sunã aikata abin da ake umarnin su)

Verse 7 — Surah At-Tahrim 66:7

Yã kũ waɗanda suka kãfirta!* Kada ku kãwo wani uzuri a yau. Anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa kawai ne

Verse 8 — Surah At-Tahrim 66:8

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi *da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne

Verse 9 — Surah At-Tahrim 66:9

Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita

Verse 10 — Surah At-Tahrim 66:10

Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta*: mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyin Mu sãlihai, sai suka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga

Verse 11 — Surah At-Tahrim 66:11

Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna,* sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurin Ka a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai

Verse 12 — Surah At-Tahrim 66:12

Da Maryama* ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da Littattafan Sa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u