Back to Languages

Hausa - Chapter 7 - Al-Araf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Araf 7:1

Verse 2 — Surah Al-Araf 7:2

Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai

Verse 3 — Surah Al-Araf 7:3

Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa

Verse 4 — Surah Al-Araf 7:4

Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla

Verse 5 — Surah Al-Araf 7:5

Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci

Verse 6 — Surah Al-Araf 7:6

Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin

Verse 7 — Surah Al-Araf 7:7

Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba

Verse 8 — Surah Al-Araf 7:8

Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara

Verse 9 — Surah Al-Araf 7:9

Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci

Verse 10 — Surah Al-Araf 7:10

Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa

Verse 11 — Surah Al-Araf 7:11

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba

Verse 12 — Surah Al-Araf 7:12

Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka

Verse 13 — Surah Al-Araf 7:13

Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci

Verse 14 — Surah Al-Araf 7:14

Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar* da su

Verse 15 — Surah Al-Araf 7:15

Ya ce: "Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri

Verse 16 — Surah Al-Araf 7:16

Ya ce: "To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici

Verse 17 — Surah Al-Araf 7:17

Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba

Verse 18 — Surah Al-Araf 7:18

Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya

Verse 19 — Surah Al-Araf 7:19

Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga Azzãlumai

Verse 20 — Surah Al-Araf 7:20

Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama

Verse 21 — Surah Al-Araf 7:21

Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne

Verse 22 — Surah Al-Araf 7:22

Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne

Verse 23 — Surah Al-Araf 7:23

Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra

Verse 24 — Surah Al-Araf 7:24

Ya ce: "Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi

Verse 25 — Surah Al-Araf 7:25

Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku

Verse 26 — Surah Al-Araf 7:26

Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa* a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa

Verse 27 — Surah Al-Araf 7:27

Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni

Verse 28 — Surah Al-Araf 7:28

Kuma idan suka aikata alfãsha* su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah

Verse 29 — Surah Al-Araf 7:29

Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa

Verse 30 — Surah Al-Araf 7:30

Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne

Verse 31 — Surah Al-Araf 7:31

Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna

Verse 32 — Surah Al-Araf 7:32

Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani

Verse 33 — Surah Al-Araf 7:33

Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah

Verse 34 — Surah Al-Araf 7:34

Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba

Verse 35 — Surah Al-Araf 7:35

Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki

Verse 36 — Surah Al-Araf 7:36

Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne

Verse 37 — Surah Al-Araf 7:37

To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai

Verse 38 — Surah Al-Araf 7:38

Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane* akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba

Verse 39 — Surah Al-Araf 7:39

Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa

Verse 40 — Surah Al-Araf 7:40

Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi

Verse 41 — Surah Al-Araf 7:41

Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai

Verse 42 — Surah Al-Araf 7:42

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne

Verse 43 — Surah Al-Araf 7:43

Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 44 — Surah Al-Araf 7:44

Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai

Verse 45 — Surah Al-Araf 7:45

Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne

Verse 46 — Surah Al-Araf 7:46

Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki,* kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni

Verse 47 — Surah Al-Araf 7:47

Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne Azzãlumai

Verse 48 — Surah Al-Araf 7:48

Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku

Verse 49 — Surah Al-Araf 7:49

Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba

Verse 50 — Surah Al-Araf 7:50

Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai

Verse 51 — Surah Al-Araf 7:51

Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu

Verse 52 — Surah Al-Araf 7:52

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani

Verse 53 — Surah Al-Araf 7:53

Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu

Verse 54 — Surah Al-Araf 7:54

Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana

Verse 55 — Surah Al-Araf 7:55

Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka

Verse 56 — Surah Al-Araf 7:56

Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa

Verse 57 — Surah Al-Araf 7:57

Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi,* sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni

Verse 58 — Surah Al-Araf 7:58

Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗan da suke gõdẽwa

Verse 59 — Surah Al-Araf 7:59

Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma

Verse 60 — Surah Al-Araf 7:60

Mashawarta* daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya

Verse 61 — Surah Al-Araf 7:61

Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu

Verse 62 — Surah Al-Araf 7:62

Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba

Verse 63 — Surah Al-Araf 7:63

Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku

Verse 64 — Surah Al-Araf 7:64

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu

Verse 65 — Surah Al-Araf 7:65

Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba

Verse 66 — Surah Al-Araf 7:66

Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata

Verse 67 — Surah Al-Araf 7:67

Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu

Verse 68 — Surah Al-Araf 7:68

Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce

Verse 69 — Surah Al-Araf 7:69

Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara

Verse 70 — Surah Al-Araf 7:70

Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya

Verse 71 — Surah Al-Araf 7:71

Ya ce: "Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne

Verse 72 — Surah Al-Araf 7:72

To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba

Verse 73 — Surah Al-Araf 7:73

Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku

Verse 74 — Surah Al-Araf 7:74

Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi

Verse 75 — Surah Al-Araf 7:75

Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar*, ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: "Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne

Verse 76 — Surah Al-Araf 7:76

Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne

Verse 77 — Surah Al-Araf 7:77

Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã kasance daga manzanni

Verse 78 — Surah Al-Araf 7:78

Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne

Verse 79 — Surah Al-Araf 7:79

Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha

Verse 80 — Surah Al-Araf 7:80

Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: "Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu

Verse 81 — Surah Al-Araf 7:81

Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata

Verse 82 — Surah Al-Araf 7:82

Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki

Verse 83 — Surah Al-Araf 7:83

Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa

Verse 84 — Surah Al-Araf 7:84

Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance

Verse 85 — Surah Al-Araf 7:85

Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai

Verse 86 — Surah Al-Araf 7:86

Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacẽwa, kuma kunã kangẽwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nẽman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance

Verse 87 — Surah Al-Araf 7:87

Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci

Verse 88 — Surah Al-Araf 7:88

Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ

Verse 89 — Surah Al-Araf 7:89

Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Alah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci

Verse 90 — Surah Al-Araf 7:90

Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne

Verse 91 — Surah Al-Araf 7:91

Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidan su, sunã guggurfãne

Verse 92 — Surah Al-Araf 7:92

Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra

Verse 93 — Surah Al-Araf 7:93

Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai

Verse 94 — Surah Al-Araf 7:94

Kuma ba Mu aika wani Annabi* a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai

Verse 95 — Surah Al-Araf 7:95

Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." (sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa

Verse 96 — Surah Al-Araf 7:96

Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa

Verse 97 — Surah Al-Araf 7:97

Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci

Verse 98 — Surah Al-Araf 7:98

Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa

Verse 99 — Surah Al-Araf 7:99

Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra

Verse 100 — Surah Al-Araf 7:100

Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji

Verse 101 — Surah Al-Araf 7:101

Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai

Verse 102 — Surah Al-Araf 7:102

Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai

Verse 103 — Surah Al-Araf 7:103

Sa'an nan kuma Mun aika Musa,* daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take

Verse 104 — Surah Al-Araf 7:104

Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu

Verse 105 — Surah Al-Araf 7:105

Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni

Verse 106 — Surah Al-Araf 7:106

Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya

Verse 107 — Surah Al-Araf 7:107

Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyanan ne

Verse 108 — Surah Al-Araf 7:108

Kuma ya fizge hannun sa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi

Verse 109 — Surah Al-Araf 7:109

Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi

Verse 110 — Surah Al-Araf 7:110

Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa

Verse 111 — Surah Al-Araf 7:111

Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa

Verse 112 — Surah Al-Araf 7:112

Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi

Verse 113 — Surah Al-Araf 7:113

Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya

Verse 114 — Surah Al-Araf 7:114

Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta

Verse 115 — Surah Al-Araf 7:115

Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa

Verse 116 — Surah Al-Araf 7:116

Ya ce: "Ku jẽfa." To a õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma

Verse 117 — Surah Al-Araf 7:117

Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi

Verse 118 — Surah Al-Araf 7:118

Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci

Verse 119 — Surah Al-Araf 7:119

Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu

Verse 120 — Surah Al-Araf 7:120

Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada

Verse 121 — Surah Al-Araf 7:121

Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu

Verse 122 — Surah Al-Araf 7:122

Ubangijin Mũsã da Harũna

Verse 123 — Surah Al-Araf 7:123

Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani

Verse 124 — Surah Al-Araf 7:124

Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya

Verse 125 — Surah Al-Araf 7:125

Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne

Verse 126 — Surah Al-Araf 7:126

Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai

Verse 127 — Surah Al-Araf 7:127

Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne

Verse 128 — Surah Al-Araf 7:128

Mũsã ya ce wa mutãnensa:* "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce

Verse 129 — Surah Al-Araf 7:129

Suka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa

Verse 130 — Surah Al-Araf 7:130

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa

Verse 131 — Surah Al-Araf 7:131

Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani

Verse 132 — Surah Al-Araf 7:132

Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba

Verse 133 — Surah Al-Araf 7:133

Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa*; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi

Verse 134 — Surah Al-Araf 7:134

Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai

Verse 135 — Surah Al-Araf 7:135

To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa

Verse 136 — Surah Al-Araf 7:136

Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai

Verse 137 — Surah Al-Araf 7:137

Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa

Verse 138 — Surah Al-Araf 7:138

Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa "* Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta

Verse 139 — Surah Al-Araf 7:139

Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne

Verse 140 — Surah Al-Araf 7:140

Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu

Verse 141 — Surah Al-Araf 7:141

Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku,* Mai girma

Verse 142 — Surah Al-Araf 7:142

Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin* kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi

Verse 143 — Surah Al-Araf 7:143

Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai

Verse 144 — Surah Al-Araf 7:144

Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya

Verse 145 — Surah Al-Araf 7:145

Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu;* zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai

Verse 146 — Surah Al-Araf 7:146

Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai

Verse 147 — Surah Al-Araf 7:147

Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa

Verse 148 — Surah Al-Araf 7:148

Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi*, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci

Verse 149 — Surah Al-Araf 7:149

Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra

Verse 150 — Surah Al-Araf 7:150

Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne Azzãlumai

Verse 151 — Surah Al-Araf 7:151

Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama

Verse 152 — Surah Al-Araf 7:152

Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya

Verse 153 — Surah Al-Araf 7:153

Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai

Verse 154 — Surah Al-Araf 7:154

Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne

Verse 155 — Surah Al-Araf 7:155

Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara

Verse 156 — Surah Al-Araf 7:156

Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyin Mu mũminai ne

Verse 157 — Surah Al-Araf 7:157

Waɗanda suke sunã bin Manzo*, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alhẽri, kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yana halatta musu abũ- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tãre da shi, waɗan- nan ne mãsu cin nasara

Verse 158 — Surah Al-Araf 7:158

Ka ce: "Yã kũ mutãne!* Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa

Verse 159 — Surah Al-Araf 7:159

Kuma daga mutãnen* Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci

Verse 160 — Surah Al-Araf 7:160

Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen* da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta

Verse 161 — Surah Al-Araf 7:161

Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya*, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa

Verse 162 — Surah Al-Araf 7:162

Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana* watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci

Verse 163 — Surah Al-Araf 7:163

Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar* ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci

Verse 164 — Surah Al-Araf 7:164

Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa

Verse 165 — Surah Al-Araf 7:165

To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci

Verse 166 — Surah Al-Araf 7:166

Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu

Verse 167 — Surah Al-Araf 7:167

Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai

Verse 168 — Surah Al-Araf 7:168

Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa

Verse 169 — Surah Al-Araf 7:169

Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar* wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba

Verse 170 — Surah Al-Araf 7:170

Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa

Verse 171 — Surah Al-Araf 7:171

Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse* sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa

Verse 172 — Surah Al-Araf 7:172

Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne

Verse 173 — Surah Al-Araf 7:173

Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata

Verse 174 — Surah Al-Araf 7:174

Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa

Verse 175 — Surah Al-Araf 7:175

Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa* ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku

Verse 176 — Surah Al-Araf 7:176

Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni

Verse 177 — Surah Al-Araf 7:177

Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta

Verse 178 — Surah Al-Araf 7:178

Wanda* Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra

Verse 179 — Surah Al-Araf 7:179

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu

Verse 180 — Surah Al-Araf 7:180

Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau.* Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa

Verse 181 — Surah Al-Araf 7:181

Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci

Verse 182 — Surah Al-Araf 7:182

Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba

Verse 183 — Surah Al-Araf 7:183

Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne

Verse 184 — Surah Al-Araf 7:184

Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu?* shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa

Verse 185 — Surah Al-Araf 7:185

Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni

Verse 186 — Surah Al-Araf 7:186

Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa

Verse 187 — Surah Al-Araf 7:187

Sunã tambayar ka* daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani

Verse 188 — Surah Al-Araf 7:188

Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni

Verse 189 — Surah Al-Araf 7:189

Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare* ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya

Verse 190 — Surah Al-Araf 7:190

To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki

Verse 191 — Surah Al-Araf 7:191

Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa

Verse 192 — Surah Al-Araf 7:192

Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka

Verse 193 — Surah Al-Araf 7:193

Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne

Verse 194 — Surah Al-Araf 7:194

Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya

Verse 195 — Surah Al-Araf 7:195

Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan* shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini

Verse 196 — Surah Al-Araf 7:196

Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai

Verse 197 — Surah Al-Araf 7:197

Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka

Verse 198 — Surah Al-Araf 7:198

Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani

Verse 199 — Surah Al-Araf 7:199

Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai

Verse 200 — Surah Al-Araf 7:200

Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani

Verse 201 — Surah Al-Araf 7:201

Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra

Verse 202 — Surah Al-Araf 7:202

Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa

Verse 203 — Surah Al-Araf 7:203

Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni

Verse 204 — Surah Al-Araf 7:204

Kuma idan an karanta* Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama

Verse 205 — Surah Al-Araf 7:205

Kuma ka ambaci* Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu

Verse 206 — Surah Al-Araf 7:206

Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada