Back to Languages

Hausa - Chapter 9 - At-Tawbah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 109 — Surah At-Tawbah 9:109

Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne Azzãlumai