Back to Languages

Hausa - Chapter 9 - At-Tawbah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 118 — Surah At-Tawbah 9:118

Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun* nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai