Back to Languages

Hausa - Chapter 9 - At-Tawbah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 34 — Surah At-Tawbah 9:34

Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr* da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi