Back to Languages

Hausa - Chapter 9 - At-Tawbah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 70 — Surah At-Tawbah 9:70

Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta