Back to Languages

Hausa - Chapter 9 - At-Tawbah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 71 — Surah At-Tawbah 9:71

Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri* kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima