Back to Languages

Hausa - Chapter 87 - Al-Ala

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Ala 87:1

Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi ɗaukaka

Verse 2 — Surah Al-Ala 87:2

Wanda Ya yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar

Verse 3 — Surah Al-Ala 87:3

Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alheri da ta sharri)

Verse 4 — Surah Al-Ala 87:4

Kuma Wanda Ya fitar da makiyaya

Verse 5 — Surah Al-Ala 87:5

Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa

Verse 6 — Surah Al-Ala 87:6

Za mu karantar da kai (Alƙur'ani) saboda haka ba za ka manta (shi) ba

Verse 7 — Surah Al-Ala 87:7

Face abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake boye

Verse 8 — Surah Al-Ala 87:8

Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi

Verse 9 — Surah Al-Ala 87:9

Saboda baka, ka tunatar, idan tunatarwa za ta yi amfani

Verse 10 — Surah Al-Ala 87:10

Wanda yake tsoron (Allah) Zai tuna

Verse 11 — Surah Al-Ala 87:11

Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta

Verse 12 — Surah Al-Ala 87:12

Wanda zai shiga wutar da ta fi girma

Verse 13 — Surah Al-Ala 87:13

Sa'an nan ba zai mutu ba a cikinta, kuma ba zai rayu ba

Verse 14 — Surah Al-Ala 87:14

Lalle ne wanda ya tsarkaka (da imani) ya samu babban rabo

Verse 15 — Surah Al-Ala 87:15

Kuma ya ambaci sunan* Ubangijinsa, sa'an nan ya yi salla

Verse 16 — Surah Al-Ala 87:16

Ba haka ba! Kuna zaɓin rayuwa ta kusa duniya

Verse 17 — Surah Al-Ala 87:17

Alhali Lahira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa

Verse 18 — Surah Al-Ala 87:18

Lalle ne, wannan* yana a cikin littafan farko

Verse 19 — Surah Al-Ala 87:19

Littaffan Ibrahim da Musa