Verse 1 — Surah Al-Fatiha 1:1
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai
Verse 2 — Surah Al-Fatiha 1:2
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu
Verse 3 — Surah Al-Fatiha 1:3
Mai rahama, Mai jin ƙai
Verse 4 — Surah Al-Fatiha 1:4
Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako
Verse 5 — Surah Al-Fatiha 1:5
Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa
Verse 6 — Surah Al-Fatiha 1:6
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya
Verse 7 — Surah Al-Fatiha 1:7
Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba