Verse 1 — Surah An-Nas 114:1
Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne
Verse 2 — Surah An-Nas 114:2
Mamallakin mutane
Verse 3 — Surah An-Nas 114:3
Abin bautãwar mutãne
Verse 4 — Surah An-Nas 114:4
Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa
Verse 5 — Surah An-Nas 114:5
Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane
Verse 6 — Surah An-Nas 114:6
Daga aljannu da mutane