Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau
Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya
A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu*! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu
Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi wanin Sa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan
Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah
Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamar Sa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku
Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba
Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su
Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin* su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin**. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum
Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu* sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu
Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijĩna* ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan."Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa** ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu
Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya
Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganin Sa da jin Sa! Bã su da wani majiɓinci baicin Sa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa
Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa
Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardar Sa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya.* Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncin Mu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna
Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu
Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa
Kuma ka buga musu misãli* da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin)
Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a
Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma
Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum
Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya
To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi
Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra* wani da Ubangijina ba
Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme
Dũkiya da ɗiya,* sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri
Kuma a gittã* su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba
Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa
Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai
Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba
Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa* (Mahalaka) a tsakãninsu
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli
Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko* ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i
Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyi Na da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada
Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa
(Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki
Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa, kã zo da wani babban abu
Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma
Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa
Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki* a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce
Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum* ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa
Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: "Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu
Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau*, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu
Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu
Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa
Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin* Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce
Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa*, majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai
Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo* ba a Rãnar ¡iyãma
Ka ce: "Dã tẽku* ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari
Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa