Back to Languages

Hausa - Chapter 19 - Maryam

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Maryam 19:1

Verse 2 — Surah Maryam 19:2

Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya

Verse 3 — Surah Maryam 19:3

A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye

Verse 4 — Surah Maryam 19:4

Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji

Verse 5 — Surah Maryam 19:5

Kuma lalle nĩ, na ji tsõron* dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa

Verse 6 — Surah Maryam 19:6

Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji

Verse 7 — Surah Maryam 19:7

(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni

Verse 8 — Surah Maryam 19:8

Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa

Verse 9 — Surah Maryam 19:9

Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba

Verse 10 — Surah Maryam 19:10

Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai

Verse 11 — Surah Maryam 19:11

Sai ya fita ga mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma

Verse 12 — Surah Maryam 19:12

Yã kai Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro

Verse 13 — Surah Maryam 19:13

Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gun Mu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa

Verse 14 — Surah Maryam 19:14

Kuma mai biyayya ga mahaifan sa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba

Verse 15 — Surah Maryam 19:15

Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai

Verse 16 — Surah Maryam 19:16

Kuma ka ambaci Maryamu* a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas

Verse 17 — Surah Maryam 19:17

Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci

Verse 18 — Surah Maryam 19:18

Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini

Verse 19 — Surah Maryam 19:19

Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki

Verse 20 — Surah Maryam 19:20

Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba

Verse 21 — Surah Maryam 19:21

Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi* ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce

Verse 22 — Surah Maryam 19:22

Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa

Verse 23 — Surah Maryam 19:23

Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta

Verse 24 — Surah Maryam 19:24

Sai (yãron da ta haifa) ya* kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki

Verse 25 — Surah Maryam 19:25

Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu

Verse 26 — Surah Maryam 19:26

Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki*. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba

Verse 27 — Surah Maryam 19:27

Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma

Verse 28 — Surah Maryam 19:28

Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba

Verse 29 — Surah Maryam 19:29

Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri

Verse 30 — Surah Maryam 19:30

Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi

Verse 31 — Surah Maryam 19:31

Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai

Verse 32 — Surah Maryam 19:32

Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri

Verse 33 — Surah Maryam 19:33

Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai

Verse 34 — Surah Maryam 19:34

Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta

Verse 35 — Surah Maryam 19:35

Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã*. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa

Verse 36 — Surah Maryam 19:36

Kuma lalle Allah ne Ubangijina* kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici

Verse 37 — Surah Maryam 19:37

Sai ƙungiyõyin* suka sãɓã wa jũna a tsakãnins u. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma

Verse 38 — Surah Maryam 19:38

Mẽne ne ya yi jinsu*, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna

Verse 39 — Surah Maryam 19:39

Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni

Verse 40 — Surah Maryam 19:40

Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa* da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su

Verse 41 — Surah Maryam 19:41

Kuma ambaci Ibrãhĩm* a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi

Verse 42 — Surah Maryam 19:42

A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka

Verse 43 — Surah Maryam 19:43

Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici

Verse 44 — Surah Maryam 19:44

Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama

Verse 45 — Surah Maryam 19:45

Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan

Verse 46 — Surah Maryam 19:46

Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci

Verse 47 — Surah Maryam 19:47

Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka.* Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni

Verse 48 — Surah Maryam 19:48

Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina

Verse 49 — Surah Maryam 19:49

To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi

Verse 50 — Surah Maryam 19:50

Kuma Muka yi musu kyauta daga Rahamar Mu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya* maɗaukaki

Verse 51 — Surah Maryam 19:51

Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi

Verse 52 — Surah Maryam 19:52

Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa

Verse 53 — Surah Maryam 19:53

Kuma Muka yi masa kyauta daga Rahamar Mu da ɗan'uwan sa Hãrũna, ya zama Annabi

Verse 54 — Surah Maryam 19:54

Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi

Verse 55 — Surah Maryam 19:55

Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens *da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa

Verse 56 — Surah Maryam 19:56

Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi

Verse 57 — Surah Maryam 19:57

Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki

Verse 58 — Surah Maryam 19:58

Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka

Verse 59 — Surah Maryam 19:59

Sai waɗansu 'yan bãya* suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri

Verse 60 — Surah Maryam 19:60

Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme

Verse 61 — Surah Maryam 19:61

Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa

Verse 62 — Surah Maryam 19:62

Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice

Verse 63 — Surah Maryam 19:63

Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa

Verse 64 — Surah Maryam 19:64

(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka* Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma** (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba)

Verse 65 — Surah Maryam 19:65

Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãnin su. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautar sa. Shin kã san wani takwara a gare shi

Verse 66 — Surah Maryam 19:66

Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai

Verse 67 — Surah Maryam 19:67

Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba

Verse 68 — Surah Maryam 19:68

To, Munã rantsuwa da Ubangijin ka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne

Verse 69 — Surah Maryam 19:69

Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya

Verse 70 — Surah Maryam 19:70

Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗan da suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita

Verse 71 — Surah Maryam 19:71

Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata.* Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce

Verse 72 — Surah Maryam 19:72

Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne

Verse 73 — Surah Maryam 19:73

Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa

Verse 74 — Surah Maryam 19:74

Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã

Verse 75 — Surah Maryam 19:75

Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna

Verse 76 — Surah Maryam 19:76

Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma

Verse 77 — Surah Maryam 19:77

Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya

Verse 78 — Surah Maryam 19:78

Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne

Verse 79 — Surah Maryam 19:79

Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa

Verse 80 — Surah Maryam 19:80

Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai

Verse 81 — Surah Maryam 19:81

Kuma suka riƙi gumãka,* baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su

Verse 82 — Surah Maryam 19:82

Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu

Verse 83 — Surah Maryam 19:83

Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu* a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa

Verse 84 — Surah Maryam 19:84

Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar Ajali ne kawai, ƙidãyãwa

Verse 85 — Surah Maryam 19:85

A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma

Verse 86 — Surah Maryam 19:86

Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa

Verse 87 — Surah Maryam 19:87

Ba su malakar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama

Verse 88 — Surah Maryam 19:88

Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã

Verse 89 — Surah Maryam 19:89

Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni

Verse 90 — Surah Maryam 19:90

Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu

Verse 91 — Surah Maryam 19:91

Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama

Verse 92 — Surah Maryam 19:92

Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã

Verse 93 — Surah Maryam 19:93

Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã

Verse 94 — Surah Maryam 19:94

Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya

Verse 95 — Surah Maryam 19:95

Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai

Verse 96 — Surah Maryam 19:96

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so

Verse 97 — Surah Maryam 19:97

Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma

Verse 98 — Surah Maryam 19:98

Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu