Back to Languages

Hausa - Chapter 20 - Ta-Ha

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ta-Ha 20:1

Verse 2 — Surah Ta-Ha 20:2

Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba

Verse 3 — Surah Ta-Ha 20:3

Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah

Verse 4 — Surah Ta-Ha 20:4

(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka

Verse 5 — Surah Ta-Ha 20:5

Mai rahama, Ya daidaita* a kan Al'arshi

Verse 6 — Surah Ta-Ha 20:6

Abin da yake a cikin sammai nãsa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya

Verse 7 — Surah Ta-Ha 20:7

Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa

Verse 8 — Surah Ta-Ha 20:8

Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau

Verse 9 — Surah Ta-Ha 20:9

Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka

Verse 10 — Surah Ta-Ha 20:10

A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar

Verse 11 — Surah Ta-Ha 20:11

Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã

Verse 12 — Surah Ta-Ha 20:12

Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka* Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa

Verse 13 — Surah Ta-Ha 20:13

Kuma Nĩ nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi

Verse 14 — Surah Ta-Ha 20:14

Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni

Verse 15 — Surah Ta-Ha 20:15

Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa

Verse 16 — Surah Ta-Ha 20:16

Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka

Verse 17 — Surah Ta-Ha 20:17

Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa

Verse 18 — Surah Ta-Ha 20:18

Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci* na dabam a gare ta

Verse 19 — Surah Ta-Ha 20:19

Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã

Verse 20 — Surah Ta-Ha 20:20

Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa

Verse 21 — Surah Ta-Ha 20:21

Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko

Verse 22 — Surah Ta-Ha 20:22

Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam

Verse 23 — Surah Ta-Ha 20:23

Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyin Mu manya

Verse 24 — Surah Ta-Ha 20:24

Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)

Verse 25 — Surah Ta-Ha 20:25

Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa* mini, ƙirjĩna

Verse 26 — Surah Ta-Ha 20:26

kuma ka sawwake mun Al'amari na

Verse 27 — Surah Ta-Ha 20:27

Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna

Verse 28 — Surah Ta-Ha 20:28

Su fahimci maganãta

Verse 29 — Surah Ta-Ha 20:29

Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena

Verse 30 — Surah Ta-Ha 20:30

Verse 31 — Surah Ta-Ha 20:31

Ka ƙarfafa halittata da shi

Verse 32 — Surah Ta-Ha 20:32

Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina

Verse 33 — Surah Ta-Ha 20:33

Dõmin mu tsarkake Ka da yawa

Verse 34 — Surah Ta-Ha 20:34

Kuma mu tuna Ka da yawa

Verse 35 — Surah Ta-Ha 20:35

Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu

Verse 36 — Surah Ta-Ha 20:36

Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã

Verse 37 — Surah Ta-Ha 20:37

Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam

Verse 38 — Surah Ta-Ha 20:38

A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka

Verse 39 — Surah Ta-Ha 20:39

Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan gan iNa

Verse 40 — Surah Ta-Ha 20:40

A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi* kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã

Verse 41 — Surah Ta-Ha 20:41

Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina

Verse 42 — Surah Ta-Ha 20:42

Ka tafi kai da ɗan uwanka game da ãyõyi Na, kuma kada ku yi rauni ga ambatõ Na

Verse 43 — Surah Ta-Ha 20:43

Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)

Verse 44 — Surah Ta-Ha 20:44

Sai ku gaya masa magana mai laushi,* tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro

Verse 45 — Surah Ta-Ha 20:45

Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi

Verse 46 — Surah Ta-Ha 20:46

Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani

Verse 47 — Surah Ta-Ha 20:47

Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya

Verse 48 — Surah Ta-Ha 20:48

Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwa azãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya

Verse 49 — Surah Ta-Ha 20:49

Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã

Verse 50 — Surah Ta-Ha 20:50

Ya ce: "Ubangijin mu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar

Verse 51 — Surah Ta-Ha 20:51

Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko

Verse 52 — Surah Ta-Ha 20:52

Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa

Verse 53 — Surah Ta-Ha 20:53

Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi* Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam

Verse 54 — Surah Ta-Ha 20:54

Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali

Verse 55 — Surah Ta-Ha 20:55

Daga gare ta* Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam

Verse 56 — Surah Ta-Ha 20:56

Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyin Mu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya

Verse 57 — Surah Ta-Ha 20:57

Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã

Verse 58 — Surah Ta-Ha 20:58

To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa

Verse 59 — Surah Ta-Ha 20:59

Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi

Verse 60 — Surah Ta-Ha 20:60

Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo

Verse 61 — Surah Ta-Ha 20:61

Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe

Verse 62 — Surah Ta-Ha 20:62

Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãnin su kuma suka asirta gãnawa

Verse 63 — Surah Ta-Ha 20:63

Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya

Verse 64 — Surah Ta-Ha 20:64

Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta

Verse 65 — Surah Ta-Ha 20:65

Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa

Verse 66 — Surah Ta-Ha 20:66

Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri

Verse 67 — Surah Ta-Ha 20:67

Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa

Verse 68 — Surah Ta-Ha 20:68

Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka

Verse 69 — Surah Ta-Ha 20:69

Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je

Verse 70 — Surah Ta-Ha 20:70

Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã

Verse 71 — Surah Ta-Ha 20:71

Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)

Verse 72 — Surah Ta-Ha 20:72

Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne

Verse 73 — Surah Ta-Ha 20:73

Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kuma Mafi wanzuwa

Verse 74 — Surah Ta-Ha 20:74

Lalle* shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa

Verse 75 — Surah Ta-Ha 20:75

Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka

Verse 76 — Surah Ta-Ha 20:76

Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku

Verse 77 — Surah Ta-Ha 20:77

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riska, kuma bã ka fargabar nutsẽwa

Verse 78 — Surah Ta-Ha 20:78

Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su

Verse 79 — Surah Ta-Ha 20:79

Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba

Verse 80 — Surah Ta-Ha 20:80

Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku

Verse 81 — Surah Ta-Ha 20:81

Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har fushĩ Na ya sauka a kanku. Kuma wanda fushĩ Na ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi

Verse 82 — Surah Ta-Ha 20:82

Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa

Verse 83 — Surah Ta-Ha 20:83

Kuma mẽne ne ya gaggautar* da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã

Verse 84 — Surah Ta-Ha 20:84

Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda

Verse 85 — Surah Ta-Ha 20:85

Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su

Verse 86 — Surah Ta-Ha 20:86

Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna

Verse 87 — Surah Ta-Ha 20:87

Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka* ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa

Verse 88 — Surah Ta-Ha 20:88

Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta

Verse 89 — Surah Ta-Ha 20:89

Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni

Verse 90 — Surah Ta-Ha 20:90

Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umarnĩna

Verse 91 — Surah Ta-Ha 20:91

Suka ce ba zamu gushe ba muna bauta a gareshi ba har sai Musa dawo

Verse 92 — Surah Ta-Ha 20:92

(Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace

Verse 93 — Surah Ta-Ha 20:93

Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umarnina ne

Verse 94 — Surah Ta-Ha 20:94

(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba

Verse 95 — Surah Ta-Ha 20:95

(Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Kai Sãmiri

Verse 96 — Surah Ta-Ha 20:96

(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini

Verse 97 — Surah Ta-Ha 20:97

(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi,* sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa

Verse 98 — Surah Ta-Ha 20:98

Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci* dukkan kõme da ilmi

Verse 99 — Surah Ta-Ha 20:99

Kamar wancan ne Muke lãbartãwa* a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gun Mu

Verse 100 — Surah Ta-Ha 20:100

Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanã ɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma

Verse 101 — Surah Ta-Ha 20:101

Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma

Verse 102 — Surah Ta-Ha 20:102

A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu

Verse 103 — Surah Ta-Ha 20:103

Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma

Verse 104 — Surah Ta-Ha 20:104

Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda

Verse 105 — Surah Ta-Ha 20:105

Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu* sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa

Verse 106 — Surah Ta-Ha 20:106

Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi

Verse 107 — Surah Ta-Ha 20:107

Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu

Verse 108 — Surah Ta-Ha 20:108

A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya

Verse 109 — Surah Ta-Ha 20:109

A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da ya yi magana

Verse 110 — Surah Ta-Ha 20:110

Yanã sanin* abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani

Verse 111 — Surah Ta-Ha 20:111

Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe

Verse 112 — Surah Ta-Ha 20:112

Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa

Verse 113 — Surah Ta-Ha 20:113

Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa

Verse 114 — Surah Ta-Ha 20:114

Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa* da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi

Verse 115 — Surah Ta-Ha 20:115

Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shi ba

Verse 116 — Surah Ta-Ha 20:116

Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya

Verse 117 — Surah Ta-Ha 20:117

Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi* ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala

Verse 118 — Surah Ta-Ha 20:118

Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba

Verse 119 — Surah Ta-Ha 20:119

Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba

Verse 120 — Surah Ta-Ha 20:120

Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa

Verse 121 — Surah Ta-Ha 20:121

Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace

Verse 122 — Surah Ta-Ha 20:122

Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi)

Verse 123 — Surah Ta-Ha 20:123

Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala

Verse 124 — Surah Ta-Ha 20:124

Kuma wanda ya bijire* daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho

Verse 125 — Surah Ta-Ha 20:125

Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani

Verse 126 — Surah Ta-Ha 20:126

Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyin Mu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka

Verse 127 — Surah Ta-Ha 20:127

Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa

Verse 128 — Surah Ta-Ha 20:128

Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula

Verse 129 — Surah Ta-Ha 20:129

Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta

Verse 130 — Surah Ta-Ha 20:130

Sai ka yi haƙuri* a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda

Verse 131 — Surah Ta-Ha 20:131

Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikin sa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa

Verse 132 — Surah Ta-Ha 20:132

Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani Arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa

Verse 133 — Surah Ta-Ha 20:133

Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba

Verse 134 — Surah Ta-Ha 20:134

Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu

Verse 135 — Surah Ta-Ha 20:135

Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa