Back to Languages

Hausa - Chapter 21 - Al-Anbiya

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Anbiya 21:1

Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa

Verse 2 — Surah Al-Anbiya 21:2

Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa

Verse 3 — Surah Al-Anbiya 21:3

Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta

Verse 4 — Surah Al-Anbiya 21:4

Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani

Verse 5 — Surah Al-Anbiya 21:5

Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko

Verse 6 — Surah Al-Anbiya 21:6

Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni

Verse 7 — Surah Al-Anbiya 21:7

Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato* idan kun kasance ba ku sani ba

Verse 8 — Surah Al-Anbiya 21:8

Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba

Verse 9 — Surah Al-Anbiya 21:9

Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa

Verse 10 — Surah Al-Anbiya 21:10

Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku,* a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta

Verse 11 — Surah Al-Anbiya 21:11

Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta

Verse 12 — Surah Al-Anbiya 21:12

Sai a lõkacin da suka hangi azãbar Mu, sai gã su sunã gudu daga gare ta

Verse 13 — Surah Al-Anbiya 21:13

Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku

Verse 14 — Surah Al-Anbiya 21:14

Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci

Verse 15 — Surah Al-Anbiya 21:15

Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu

Verse 16 — Surah Al-Anbiya 21:16

Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba

Verse 17 — Surah Al-Anbiya 21:17

Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun* riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa

Verse 18 — Surah Al-Anbiya 21:18

Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa

Verse 19 — Surah Al-Anbiya 21:19

Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurin Sa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdar Sa. kuma bã su gajiya

Verse 20 — Surah Al-Anbiya 21:20

Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni

Verse 21 — Surah Al-Anbiya 21:21

Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)

Verse 22 — Surah Al-Anbiya 21:22

Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa

Verse 23 — Surah Al-Anbiya 21:23

Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su

Verse 24 — Surah Al-Anbiya 21:24

Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne

Verse 25 — Surah Al-Anbiya 21:25

Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini

Verse 26 — Surah Al-Anbiya 21:26

Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja

Verse 27 — Surah Al-Anbiya 21:27

Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurnin Sa suke aiki

Verse 28 — Surah Al-Anbiya 21:28

Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõron Sa

Verse 29 — Surah Al-Anbiya 21:29

Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai

Verse 30 — Surah Al-Anbiya 21:30

Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,* sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba

Verse 31 — Surah Al-Anbiya 21:31

Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa

Verse 32 — Surah Al-Anbiya 21:32

Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne

Verse 33 — Surah Al-Anbiya 21:33

Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu* a cikin wani sarari suKe iyo

Verse 34 — Surah Al-Anbiya 21:34

Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama

Verse 35 — Surah Al-Anbiya 21:35

Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku

Verse 36 — Surah Al-Anbiya 21:36

Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne

Verse 37 — Surah Al-Anbiya 21:37

An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa

Verse 38 — Surah Al-Anbiya 21:38

Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya

Verse 39 — Surah Al-Anbiya 21:39

Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba

Verse 40 — Surah Al-Anbiya 21:40

Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba

Verse 41 — Surah Al-Anbiya 21:41

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su

Verse 42 — Surah Al-Anbiya 21:42

Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu

Verse 43 — Surah Al-Anbiya 21:43

Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su* ba daga gare Mu

Verse 44 — Surah Al-Anbiya 21:44

Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage* ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya

Verse 45 — Surah Al-Anbiya 21:45

Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi

Verse 46 — Surah Al-Anbiya 21:46

Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci

Verse 47 — Surah Al-Anbiya 21:47

Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi

Verse 48 — Surah Al-Anbiya 21:48

Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa

Verse 49 — Surah Al-Anbiya 21:49

Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a

Verse 50 — Surah Al-Anbiya 21:50

Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi

Verse 51 — Surah Al-Anbiya 21:51

Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi

Verse 52 — Surah Al-Anbiya 21:52

Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu

Verse 53 — Surah Al-Anbiya 21:53

Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu

Verse 54 — Surah Al-Anbiya 21:54

Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananne

Verse 55 — Surah Al-Anbiya 21:55

Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãsu wãsã ne

Verse 56 — Surah Al-Anbiya 21:56

Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka

Verse 57 — Surah Al-Anbiya 21:57

Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya

Verse 58 — Surah Al-Anbiya 21:58

Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi

Verse 59 — Surah Al-Anbiya 21:59

Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai

Verse 60 — Surah Al-Anbiya 21:60

Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm

Verse 61 — Surah Al-Anbiya 21:61

Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida

Verse 62 — Surah Al-Anbiya 21:62

Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm

Verse 63 — Surah Al-Anbiya 21:63

Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana

Verse 64 — Surah Al-Anbiya 21:64

Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai

Verse 65 — Surah Al-Anbiya 21:65

Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana

Verse 66 — Surah Al-Anbiya 21:66

Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah

Verse 67 — Surah Al-Anbiya 21:67

Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta

Verse 68 — Surah Al-Anbiya 21:68

Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa

Verse 69 — Surah Al-Anbiya 21:69

Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm

Verse 70 — Surah Al-Anbiya 21:70

Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra

Verse 71 — Surah Al-Anbiya 21:71

Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai

Verse 72 — Surah Al-Anbiya 21:72

Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai

Verse 73 — Surah Al-Anbiya 21:73

Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurnin Mu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu

Verse 74 — Surah Al-Anbiya 21:74

Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai

Verse 75 — Surah Al-Anbiya 21:75

Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai

Verse 76 — Surah Al-Anbiya 21:76

Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma

Verse 77 — Surah Al-Anbiya 21:77

Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya

Verse 78 — Surah Al-Anbiya 21:78

Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu

Verse 79 — Surah Al-Anbiya 21:79

Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar)* ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa

Verse 80 — Surah Al-Anbiya 21:80

Kuma Muka sanar da shi sana'ar* wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne

Verse 81 — Surah Al-Anbiya 21:81

Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme

Verse 82 — Surah Al-Anbiya 21:82

Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su

Verse 83 — Surah Al-Anbiya 21:83

Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama

Verse 84 — Surah Al-Anbiya 21:84

Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurin Mu da tunãtarwa* ga mãsu ibãda

Verse 85 — Surah Al-Anbiya 21:85

Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri

Verse 86 — Surah Al-Anbiya 21:86

Kuma Muka shigar da su a cikin rahamar Mu. Lalle ne, sunã daga sãlihai

Verse 87 — Surah Al-Anbiya 21:87

Kuma mai kifi* a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai

Verse 88 — Surah Al-Anbiya 21:88

Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni

Verse 89 — Surah Al-Anbiya 21:89

Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo

Verse 90 — Surah Al-Anbiya 21:90

Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata* masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu

Verse 91 — Surah Al-Anbiya 21:91

Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.* Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya

Verse 92 — Surah Al-Anbiya 21:92

Lalle ne wannan* ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini

Verse 93 — Surah Al-Anbiya 21:93

Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni

Verse 94 — Surah Al-Anbiya 21:94

Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne

Verse 95 — Surah Al-Anbiya 21:95

Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa

Verse 96 — Surah Al-Anbiya 21:96

Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa

Verse 97 — Surah Al-Anbiya 21:97

Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci

Verse 98 — Surah Al-Anbiya 21:98

(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin* da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne

Verse 99 — Surah Al-Anbiya 21:99

Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne

Verse 100 — Surah Al-Anbiya 21:100

Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme

Verse 101 — Surah Al-Anbiya 21:101

Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne

Verse 102 — Surah Al-Anbiya 21:102

Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa

Verse 103 — Surah Al-Anbiya 21:103

Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi

Verse 104 — Surah Al-Anbiya 21:104

A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon* halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa

Verse 105 — Surah Al-Anbiya 21:105

Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato* (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩna sãlihai, sunã gãdonta

Verse 106 — Surah Al-Anbiya 21:106

Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta* ga waɗansu mutãne mãsu ibãda)

Verse 107 — Surah Al-Anbiya 21:107

Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai

Verse 108 — Surah Al-Anbiya 21:108

Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne

Verse 109 — Surah Al-Anbiya 21:109

Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci

Verse 110 — Surah Al-Anbiya 21:110

Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa

Verse 111 — Surah Al-Anbiya 21:111

Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci

Verse 112 — Surah Al-Anbiya 21:112

Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa