Back to Languages

Hausa - Chapter 22 - Al-Hajj

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Hajj 22:1

Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar* ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma

Verse 2 — Surah Al-Hajj 22:2

A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani

Verse 3 — Surah Al-Hajj 22:3

Akwai daga mutãne* wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai

Verse 4 — Surah Al-Hajj 22:4

An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr

Verse 5 — Surah Al-Hajj 22:5

Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa

Verse 6 — Surah Al-Hajj 22:6

Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme

Verse 7 — Surah Al-Hajj 22:7

Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin alkiiyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura

Verse 8 — Surah Al-Hajj 22:8

Kuma daga mutãne akwai mai yin musu* ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba

Verse 9 — Surah Al-Hajj 22:9

Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar ¡iyãma

Verse 10 — Surah Al-Hajj 22:10

(A ce masa): "Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba

Verse 11 — Surah Al-Hajj 22:11

Kuma daga mutãne akwai mai bauta* wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna

Verse 12 — Surah Al-Hajj 22:12

Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa

Verse 13 — Surah Al-Hajj 22:13

Yanã kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfãninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abõkin zama

Verse 14 — Surah Al-Hajj 22:14

Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni* kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi

Verse 15 — Surah Al-Hajj 22:15

Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici

Verse 16 — Surah Al-Hajj 22:16

Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ãni) yanã ãyõyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yanã shiryar da wanda Yake nufi

Verse 17 — Surah Al-Hajj 22:17

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme

Verse 18 — Surah Al-Hajj 22:18

Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yanã yin sujada a gare shi, da kuma rãna da watã da taurãri da duwãtsu da itãce da dabbõbi, da kuma mãsu yawa daga mutãne? Kuma waɗansu mãsu yawa azãba tã tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulãkantar, to, bã ya da wani mai girmamãwa. Kuma Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so

Verse 19 — Surah Al-Hajj 22:19

waɗannan ƙungiyõyi biyu* ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu

Verse 20 — Surah Al-Hajj 22:20

Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fãtun jikinsu

Verse 21 — Surah Al-Hajj 22:21

Kuma sunã da waɗansu gwalmõmin dũka na baƙin ƙarfe

Verse 22 — Surah Al-Hajj 22:22

A kõyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azãbar gõbara

Verse 23 — Surah Al-Hajj 22:23

Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, anã ƙawãta su, a cikinsu, da waɗansu mundãye na zĩnãri da lu'u-lu'u. Kuma tufãfinsu a cikinsu alharĩni ne

Verse 24 — Surah Al-Hajj 22:24

Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa

Verse 25 — Surah Al-Hajj 22:25

Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar* da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi

Verse 26 — Surah Al-Hajj 22:26

Kuma a lõkacin da Muka iyãkance* wa Ibrãhim wurin ¦akin (Muka ce masa), "Kada ka haɗa kõme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake daki Na dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu tsayuwa da mãsu ruku'u da mãsu sujada

Verse 27 — Surah Al-Hajj 22:27

Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi

Verse 28 — Surah Al-Hajj 22:28

Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci

Verse 29 — Surah Al-Hajj 22:29

Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ¦ãkin nin 'yantacce

Verse 30 — Surah Al-Hajj 22:30

Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima* fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur

Verse 31 — Surah Al-Hajj 22:31

Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa

Verse 32 — Surah Al-Hajj 22:32

Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda

Verse 33 — Surah Al-Hajj 22:33

Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni* a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ¦ãkin 'yantacce ne

Verse 34 — Surah Al-Hajj 22:34

Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai

Verse 35 — Surah Al-Hajj 22:35

Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su

Verse 36 — Surah Al-Hajj 22:36

Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye* a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa

Verse 37 — Surah Al-Hajj 22:37

Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi

Verse 38 — Surah Al-Hajj 22:38

Lalle ne, Allah Yanã yin faɗa* sabõda waɗanda suka yi ĩmãni. Lalle ne Allah bã Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci

Verse 39 — Surah Al-Hajj 22:39

An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cẽwa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu

Verse 40 — Surah Al-Hajj 22:40

Waɗanda aka fitina daga gidajensu bã da wani hakki ba fãce sunã cẽwa, Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne ba, sãshensu da sãshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'õ'in (Ruhbãnãwa) dã majãmi'õ'in Nasãra da gidãjen ibãdar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwãyi

Verse 41 — Surah Al-Hajj 22:41

Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani,* kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take

Verse 42 — Surah Al-Hajj 22:42

Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu

Verse 43 — Surah Al-Hajj 22:43

Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu

Verse 44 — Surah Al-Hajj 22:44

Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa (gare su) ya kasance

Verse 45 — Surah Al-Hajj 22:45

Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka

Verse 46 — Surah Al-Hajj 22:46

Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta

Verse 47 — Surah Al-Hajj 22:47

Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini* ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa

Verse 48 — Surah Al-Hajj 22:48

Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take

Verse 49 — Surah Al-Hajj 22:49

Ka ce: "Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa

Verse 50 — Surah Al-Hajj 22:50

To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci

Verse 51 — Surah Al-Hajj 22:51

Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne

Verse 52 — Surah Al-Hajj 22:52

Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri,* sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyin Sa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima

Verse 53 — Surah Al-Hajj 22:53

Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa

Verse 54 — Surah Al-Hajj 22:54

Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya

Verse 55 — Surah Al-Hajj 22:55

Kuma waɗanda suka kãfirta bã zã su gushe ba sunã a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kõ kuwa azãbar wani yini bakarãre ta jẽ musu

Verse 56 — Surah Al-Hajj 22:56

Mulki a rãnar nan ga Allah yake, Yanã hukunci a tsakãninsu. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã a cikin gidãjen Aljannar ni'ima

Verse 57 — Surah Al-Hajj 22:57

Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyin Mu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa

Verse 58 — Surah Al-Hajj 22:58

Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa

Verse 59 — Surah Al-Hajj 22:59

Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri

Verse 60 — Surah Al-Hajj 22:60

Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara

Verse 61 — Surah Al-Hajj 22:61

Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani

Verse 62 — Surah Al-Hajj 22:62

Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma

Verse 63 — Surah Al-Hajj 22:63

Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yã saukar da ruwa* daga sama, sai ƙasa ta wãyi gari kõriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa

Verse 64 — Surah Al-Hajj 22:64

Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shi ne wadatacce, Gõdadde

Verse 65 — Surah Al-Hajj 22:65

Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hõre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirãge sunã gudãna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yanã riƙe sama dõmin kada ta fãɗi a kan ƙasa fãce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutãne haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai

Verse 66 — Surah Al-Hajj 22:66

Kuma shĩ ne wanda Ya rãya ku, sa'an nan kuma Yanã matar da ku, sa'an nan kuma Yanã rãyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kãfirci ne

Verse 67 — Surah Al-Hajj 22:67

Ga kõwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabõda haka, kada su yi maka jãyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya

Verse 68 — Surah Al-Hajj 22:68

Kuma idan sun yi maka jidãli, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatãwa

Verse 69 — Surah Al-Hajj 22:69

Allah ne zai yi hukunci a tsakãninku, a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kunã sãɓawa jũna

Verse 70 — Surah Al-Hajj 22:70

Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne

Verse 71 — Surah Al-Hajj 22:71

Kuma sunã bautãwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da bã su da wani ilmi game da shi, kuma bãbu wani mai taimako ga azzãlumai

Verse 72 — Surah Al-Hajj 22:72

Kuma idan anã karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu kanã sanin abin ƙyãma a cikin fuskõkin waɗanda suka kãfirta sunã kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karãtun ayõyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yã yi alkawarinta ga waɗanda suka kãfirta. Kuma makõmarsu ta mũnana

Verse 73 — Surah Al-Hajj 22:73

Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana

Verse 74 — Surah Al-Hajj 22:74

Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi

Verse 75 — Surah Al-Hajj 22:75

Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne.* Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani

Verse 76 — Surah Al-Hajj 22:76

Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura

Verse 77 — Surah Al-Hajj 22:77

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo

Verse 78 — Surah Al-Hajj 22:78

Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci* ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi** daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako