Back to Languages

Hausa - Chapter 23 - Al-Muminun

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Muminun 23:1

Lalle ne, Mũminai* sun sãmi babban rabõ

Verse 2 — Surah Al-Muminun 23:2

Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne

Verse 3 — Surah Al-Muminun 23:3

Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne

Verse 4 — Surah Al-Muminun 23:4

Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne

Verse 5 — Surah Al-Muminun 23:5

Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne

Verse 6 — Surah Al-Muminun 23:6

Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne

Verse 7 — Surah Al-Muminun 23:7

Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi

Verse 8 — Surah Al-Muminun 23:8

Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne

Verse 9 — Surah Al-Muminun 23:9

Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa

Verse 10 — Surah Al-Muminun 23:10

Waɗannan, sũ ne magãda

Verse 11 — Surah Al-Muminun 23:11

Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi,* su a cikinta madawwama ne

Verse 12 — Surah Al-Muminun 23:12

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka

Verse 13 — Surah Al-Muminun 23:13

Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya

Verse 14 — Surah Al-Muminun 23:14

Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyawun mãsu halittawa

Verse 15 — Surah Al-Muminun 23:15

Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne

Verse 16 — Surah Al-Muminun 23:16

Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar alkiyãma, za a iãyar da ku

Verse 17 — Surah Al-Muminun 23:17

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba

Verse 18 — Surah Al-Muminun 23:18

Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne

Verse 19 — Surah Al-Muminun 23:19

Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci

Verse 20 — Surah Al-Muminun 23:20

Da wata itãciya,* tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ

Verse 21 — Surah Al-Muminun 23:21

Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni* mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ

Verse 22 — Surah Al-Muminun 23:22

Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku

Verse 23 — Surah Al-Muminun 23:23

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba

Verse 24 — Surah Al-Muminun 23:24

Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko

Verse 25 — Surah Al-Muminun 23:25

Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci

Verse 26 — Surah Al-Muminun 23:26

Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka taimakeni Saboda mutãnena sun ƙaryatã ni

Verse 27 — Surah Al-Muminun 23:27

Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idon Mu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne

Verse 28 — Surah Al-Muminun 23:28

Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai

Verse 29 — Surah Al-Muminun 23:29

Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa

Verse 30 — Surah Al-Muminun 23:30

Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙiƙa' Mãsu jarrabãwa

Verse 31 — Surah Al-Muminun 23:31

Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu

Verse 32 — Surah Al-Muminun 23:32

Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba

Verse 33 — Surah Al-Muminun 23:33

Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã

Verse 34 — Surah Al-Muminun 23:34

Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne

Verse 35 — Surah Al-Muminun 23:35

Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da kasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne

Verse 36 — Surah Al-Muminun 23:36

Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi

Verse 37 — Surah Al-Muminun 23:37

Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,* kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba

Verse 38 — Surah Al-Muminun 23:38

Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba

Verse 39 — Surah Al-Muminun 23:39

Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni

Verse 40 — Surah Al-Muminun 23:40

Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma

Verse 41 — Surah Al-Muminun 23:41

Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai

Verse 42 — Surah Al-Muminun 23:42

Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu

Verse 43 — Surah Al-Muminun 23:43

Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba

Verse 44 — Surah Al-Muminun 23:44

Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni

Verse 45 — Surah Al-Muminun 23:45

Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyin Mu da, dalĩli bayyananne

Verse 46 — Surah Al-Muminun 23:46

Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya

Verse 47 — Surah Al-Muminun 23:47

Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne

Verse 48 — Surah Al-Muminun 23:48

Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku

Verse 49 — Surah Al-Muminun 23:49

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu* zã su shiryu

Verse 50 — Surah Al-Muminun 23:50

Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã* Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari

Verse 51 — Surah Al-Muminun 23:51

Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi* kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne

Verse 52 — Surah Al-Muminun 23:52

Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa

Verse 53 — Surah Al-Muminun 23:53

Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu,* kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su

Verse 54 — Surah Al-Muminun 23:54

To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci

Verse 55 — Surah Al-Muminun 23:55

Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya

Verse 56 — Surah Al-Muminun 23:56

Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri

Verse 57 — Surah Al-Muminun 23:57

Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu

Verse 58 — Surah Al-Muminun 23:58

Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni

Verse 59 — Surah Al-Muminun 23:59

Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki

Verse 60 — Surah Al-Muminun 23:60

Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu

Verse 61 — Surah Al-Muminun 23:61

Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri)

Verse 62 — Surah Al-Muminun 23:62

Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su

Verse 63 — Surah Al-Muminun 23:63

Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne

Verse 64 — Surah Al-Muminun 23:64

Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa

Verse 65 — Surah Al-Muminun 23:65

Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku

Verse 66 — Surah Al-Muminun 23:66

Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya

Verse 67 — Surah Al-Muminun 23:67

Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha

Verse 68 — Surah Al-Muminun 23:68

Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu

Verse 69 — Surah Al-Muminun 23:69

Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi

Verse 70 — Surah Al-Muminun 23:70

Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne

Verse 71 — Surah Al-Muminun 23:71

Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton* (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa

Verse 72 — Surah Al-Muminun 23:72

Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa

Verse 73 — Surah Al-Muminun 23:73

Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya

Verse 74 — Surah Al-Muminun 23:74

Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne

Verse 75 — Surah Al-Muminun 23:75

Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa

Verse 76 — Surah Al-Muminun 23:76

Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba* sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u

Verse 77 — Surah Al-Muminun 23:77

Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi

Verse 78 — Surah Al-Muminun 23:78

Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa

Verse 79 — Surah Al-Muminun 23:79

Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku

Verse 80 — Surah Al-Muminun 23:80

Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba

Verse 81 — Surah Al-Muminun 23:81

Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa

Verse 82 — Surah Al-Muminun 23:82

Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne

Verse 83 — Surah Al-Muminun 23:83

Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko

Verse 84 — Surah Al-Muminun 23:84

Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani

Verse 85 — Surah Al-Muminun 23:85

Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba

Verse 86 — Surah Al-Muminun 23:86

Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma

Verse 87 — Surah Al-Muminun 23:87

Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba

Verse 88 — Surah Al-Muminun 23:88

Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani

Verse 89 — Surah Al-Muminun 23:89

Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku

Verse 90 — Surah Al-Muminun 23:90

Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne

Verse 91 — Surah Al-Muminun 23:91

Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa

Verse 92 — Surah Al-Muminun 23:92

Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka

Verse 93 — Surah Al-Muminun 23:93

Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi

Verse 94 — Surah Al-Muminun 23:94

Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai

Verse 95 — Surah Al-Muminun 23:95

Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi

Verse 96 — Surah Al-Muminun 23:96

Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ ne Mafi sani game da abin da suke siffantãwa

Verse 97 — Surah Al-Muminun 23:97

Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu

Verse 98 — Surah Al-Muminun 23:98

Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni

Verse 99 — Surah Al-Muminun 23:99

Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)

Verse 100 — Surah Al-Muminun 23:100

Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su

Verse 101 — Surah Al-Muminun 23:101

Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba

Verse 102 — Surah Al-Muminun 23:102

To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo

Verse 103 — Surah Al-Muminun 23:103

Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama

Verse 104 — Surah Al-Muminun 23:104

Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne

Verse 105 — Surah Al-Muminun 23:105

Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa

Verse 106 — Surah Al-Muminun 23:106

Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwace ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu

Verse 107 — Surah Al-Muminun 23:107

Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci

Verse 108 — Surah Al-Muminun 23:108

Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana

Verse 109 — Surah Al-Muminun 23:109

Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi

Verse 110 — Surah Al-Muminun 23:110

Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõ Na kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya

Verse 111 — Surah Al-Muminun 23:111

Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo

Verse 112 — Surah Al-Muminun 23:112

Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru

Verse 113 — Surah Al-Muminun 23:113

Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa

Verse 114 — Surah Al-Muminun 23:114

Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani

Verse 115 — Surah Al-Muminun 23:115

Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba

Verse 116 — Surah Al-Muminun 23:116

Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja

Verse 117 — Surah Al-Muminun 23:117

Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara

Verse 118 — Surah Al-Muminun 23:118

Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama