Back to Languages

Hausa - Chapter 2 - Al-Baqarah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 267 — Surah Al-Baqarah 2:267

Ya ku waɗan da suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikin sa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde