Back to Languages

Hausa - Chapter 2 - Al-Baqarah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 271 — Surah Al-Baqarah 2:271

Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne