Back to Languages

Hausa - Chapter 2 - Al-Baqarah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 272 — Surah Al-Baqarah 2:272

Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku