Back to Languages

Hausa - Chapter 2 - Al-Baqarah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 285 — Surah Al-Baqarah 2:285

Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take