Back to Languages

Hausa - Chapter 2 - Al-Baqarah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 79 — Surah Al-Baqarah 2:79

To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa