A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi
To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu
Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuri Na
Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya* ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyin Sa mũminai
Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna
Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba
Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai
Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa
Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umarni (da shi)
Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa
To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku
Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu
Wanda yake a wurinsa akwai* wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi
To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)
Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye* daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu
Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama
Kuma waɗansu jama'a tara* sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa,** shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne
Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki
Ka ce: "Godiya ta tabbata ga Alah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyin Sa, waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi
Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa (Allah da wani)
Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba
Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku, kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamar Sa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi
Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita, kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: "Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya
Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyin Mu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah)
Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba* daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyin Mu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni
Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni
Kuma da rãnar* da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu
Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa
(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari,* Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa
Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyin Sa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba