Back to Languages

Hausa - Chapter 26 - Ash-Shuara

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ash-Shuara 26:1

Verse 2 — Surah Ash-Shuara 26:2

Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne

Verse 3 — Surah Ash-Shuara 26:3

Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba

Verse 4 — Surah Ash-Shuara 26:4

Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai

Verse 5 — Surah Ash-Shuara 26:5

Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa

Verse 6 — Surah Ash-Shuara 26:6

To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu

Verse 7 — Surah Ash-Shuara 26:7

Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau

Verse 8 — Surah Ash-Shuara 26:8

Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba

Verse 9 — Surah Ash-Shuara 26:9

Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama

Verse 10 — Surah Ash-Shuara 26:10

Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai

Verse 11 — Surah Ash-Shuara 26:11

Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba

Verse 12 — Surah Ash-Shuara 26:12

Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni

Verse 13 — Surah Ash-Shuara 26:13

Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci* kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna

Verse 14 — Surah Ash-Shuara 26:14

Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni

Verse 15 — Surah Ash-Shuara 26:15

Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre

Verse 16 — Surah Ash-Shuara 26:16

Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne

Verse 17 — Surah Ash-Shuara 26:17

Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu

Verse 18 — Surah Ash-Shuara 26:18

Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka

Verse 19 — Surah Ash-Shuara 26:19

Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai

Verse 20 — Surah Ash-Shuara 26:20

Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi

Verse 21 — Surah Ash-Shuara 26:21

Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni

Verse 22 — Surah Ash-Shuara 26:22

Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla

Verse 23 — Surah Ash-Shuara 26:23

Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu

Verse 24 — Surah Ash-Shuara 26:24

Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni

Verse 25 — Surah Ash-Shuara 26:25

Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba

Verse 26 — Surah Ash-Shuara 26:26

Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko

Verse 27 — Surah Ash-Shuara 26:27

Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne

Verse 28 — Surah Ash-Shuara 26:28

Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta

Verse 29 — Surah Ash-Shuara 26:29

Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru

Verse 30 — Surah Ash-Shuara 26:30

Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa

Verse 31 — Surah Ash-Shuara 26:31

Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya

Verse 32 — Surah Ash-Shuara 26:32

Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne

Verse 33 — Surah Ash-Shuara 26:33

Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo

Verse 34 — Surah Ash-Shuara 26:34

(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi

Verse 35 — Surah Ash-Shuara 26:35

Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa

Verse 36 — Surah Ash-Shuara 26:36

Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne

Verse 37 — Surah Ash-Shuara 26:37

Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani

Verse 38 — Surah Ash-Shuara 26:38

Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne

Verse 39 — Surah Ash-Shuara 26:39

Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne

Verse 40 — Surah Ash-Shuara 26:40

Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya

Verse 41 — Surah Ash-Shuara 26:41

To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya

Verse 42 — Surah Ash-Shuara 26:42

Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai

Verse 43 — Surah Ash-Shuara 26:43

Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa

Verse 44 — Surah Ash-Shuara 26:44

Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya

Verse 45 — Surah Ash-Shuara 26:45

Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya

Verse 46 — Surah Ash-Shuara 26:46

Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada

Verse 47 — Surah Ash-Shuara 26:47

Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta

Verse 48 — Surah Ash-Shuara 26:48

Ubangijin Mũsa da Hãrũna

Verse 49 — Surah Ash-Shuara 26:49

Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya

Verse 50 — Surah Ash-Shuara 26:50

Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu

Verse 51 — Surah Ash-Shuara 26:51

Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni

Verse 52 — Surah Ash-Shuara 26:52

Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã* ne

Verse 53 — Surah Ash-Shuara 26:53

Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne

Verse 54 — Surah Ash-Shuara 26:54

Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan

Verse 55 — Surah Ash-Shuara 26:55

Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne

Verse 56 — Surah Ash-Shuara 26:56

Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne

Verse 57 — Surah Ash-Shuara 26:57

Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari

Verse 58 — Surah Ash-Shuara 26:58

Da taskõki da mazauni mai kyau

Verse 59 — Surah Ash-Shuara 26:59

Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla

Verse 60 — Surah Ash-Shuara 26:60

Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã

Verse 61 — Surah Ash-Shuara 26:61

Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne

Verse 62 — Surah Ash-Shuara 26:62

Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni

Verse 63 — Surah Ash-Shuara 26:63

Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,* kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma

Verse 64 — Surah Ash-Shuara 26:64

Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can

Verse 65 — Surah Ash-Shuara 26:65

Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya

Verse 66 — Surah Ash-Shuara 26:66

Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen

Verse 67 — Surah Ash-Shuara 26:67

Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba

Verse 68 — Surah Ash-Shuara 26:68

Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai

Verse 69 — Surah Ash-Shuara 26:69

Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm

Verse 70 — Surah Ash-Shuara 26:70

A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa

Verse 71 — Surah Ash-Shuara 26:71

Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su

Verse 72 — Surah Ash-Shuara 26:72

Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira

Verse 73 — Surah Ash-Shuara 26:73

Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku

Verse 74 — Surah Ash-Shuara 26:74

Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa

Verse 75 — Surah Ash-Shuara 26:75

Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa

Verse 76 — Surah Ash-Shuara 26:76

Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa

Verse 77 — Surah Ash-Shuara 26:77

To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu

Verse 78 — Surah Ash-Shuara 26:78

Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni

Verse 79 — Surah Ash-Shuara 26:79

Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni

Verse 80 — Surah Ash-Shuara 26:80

Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni

Verse 81 — Surah Ash-Shuara 26:81

Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni

Verse 82 — Surah Ash-Shuara 26:82

Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako

Verse 83 — Surah Ash-Shuara 26:83

Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai

Verse 84 — Surah Ash-Shuara 26:84

Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutãnen ƙarshe

Verse 85 — Surah Ash-Shuara 26:85

Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima

Verse 86 — Surah Ash-Shuara 26:86

Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu

Verse 87 — Surah Ash-Shuara 26:87

Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su

Verse 88 — Surah Ash-Shuara 26:88

A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi

Verse 89 — Surah Ash-Shuara 26:89

Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki

Verse 90 — Surah Ash-Shuara 26:90

Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa

Verse 91 — Surah Ash-Shuara 26:91

Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku

Verse 92 — Surah Ash-Shuara 26:92

Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa

Verse 93 — Surah Ash-Shuara 26:93

Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu

Verse 94 — Surah Ash-Shuara 26:94

Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun

Verse 95 — Surah Ash-Shuara 26:95

Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya

Verse 96 — Surah Ash-Shuara 26:96

Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma

Verse 97 — Surah Ash-Shuara 26:97

Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna

Verse 98 — Surah Ash-Shuara 26:98

A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu

Verse 99 — Surah Ash-Shuara 26:99

Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi

Verse 100 — Surah Ash-Shuara 26:100

Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta

Verse 101 — Surah Ash-Shuara 26:101

Kuma bã mu da abõki, masõyi

Verse 102 — Surah Ash-Shuara 26:102

Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai

Verse 103 — Surah Ash-Shuara 26:103

Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba

Verse 104 — Surah Ash-Shuara 26:104

Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai

Verse 105 — Surah Ash-Shuara 26:105

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni

Verse 106 — Surah Ash-Shuara 26:106

A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba

Verse 107 — Surah Ash-Shuara 26:107

Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce

Verse 108 — Surah Ash-Shuara 26:108

To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 109 — Surah Ash-Shuara 26:109

Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu

Verse 110 — Surah Ash-Shuara 26:110

Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 111 — Surah Ash-Shuara 26:111

Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka

Verse 112 — Surah Ash-Shuara 26:112

Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa

Verse 113 — Surah Ash-Shuara 26:113

Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa

Verse 114 — Surah Ash-Shuara 26:114

Ban zama mai kõre mũminai ba

Verse 115 — Surah Ash-Shuara 26:115

Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa

Verse 116 — Surah Ash-Shuara 26:116

Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa

Verse 117 — Surah Ash-Shuara 26:117

Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni

Verse 118 — Surah Ash-Shuara 26:118

Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai

Verse 119 — Surah Ash-Shuara 26:119

Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi

Verse 120 — Surah Ash-Shuara 26:120

Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran

Verse 121 — Surah Ash-Shuara 26:121

Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba

Verse 122 — Surah Ash-Shuara 26:122

Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama

Verse 123 — Surah Ash-Shuara 26:123

Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni

Verse 124 — Surah Ash-Shuara 26:124

A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba

Verse 125 — Surah Ash-Shuara 26:125

Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce

Verse 126 — Surah Ash-Shuara 26:126

Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 127 — Surah Ash-Shuara 26:127

Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu

Verse 128 — Surah Ash-Shuara 26:128

Shin, kunã yin ginin sitadiyo* a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa

Verse 129 — Surah Ash-Shuara 26:129

Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama

Verse 130 — Surah Ash-Shuara 26:130

Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa

Verse 131 — Surah Ash-Shuara 26:131

To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 132 — Surah Ash-Shuara 26:132

Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani

Verse 133 — Surah Ash-Shuara 26:133

Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya

Verse 134 — Surah Ash-Shuara 26:134

Da gõnaki da marẽmari

Verse 135 — Surah Ash-Shuara 26:135

Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma

Verse 136 — Surah Ash-Shuara 26:136

Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba

Verse 137 — Surah Ash-Shuara 26:137

Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen* mutãnen farko

Verse 138 — Surah Ash-Shuara 26:138

Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba

Verse 139 — Surah Ash-Shuara 26:139

Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba

Verse 140 — Surah Ash-Shuara 26:140

Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai

Verse 141 — Surah Ash-Shuara 26:141

Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni

Verse 142 — Surah Ash-Shuara 26:142

A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba

Verse 143 — Surah Ash-Shuara 26:143

Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce

Verse 144 — Surah Ash-Shuara 26:144

Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 145 — Surah Ash-Shuara 26:145

Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu

Verse 146 — Surah Ash-Shuara 26:146

Shin, anã barin ku* a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu

Verse 147 — Surah Ash-Shuara 26:147

A cikin gõnaki da marẽmari

Verse 148 — Surah Ash-Shuara 26:148

Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi* mãsu narkẽwa a ciki

Verse 149 — Surah Ash-Shuara 26:149

Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari

Verse 150 — Surah Ash-Shuara 26:150

Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 151 — Surah Ash-Shuara 26:151

Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata

Verse 152 — Surah Ash-Shuara 26:152

Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa

Verse 153 — Surah Ash-Shuara 26:153

Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake

Verse 154 — Surah Ash-Shuara 26:154

Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya

Verse 155 — Surah Ash-Shuara 26:155

Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan* yini, kuma kunã da shan yini sasanne

Verse 156 — Surah Ash-Shuara 26:156

Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku

Verse 157 — Surah Ash-Shuara 26:157

Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma

Verse 158 — Surah Ash-Shuara 26:158

Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba

Verse 159 — Surah Ash-Shuara 26:159

Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai

Verse 160 — Surah Ash-Shuara 26:160

Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni

Verse 161 — Surah Ash-Shuara 26:161

A lõkacin da ɗan'uwansu,* Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba

Verse 162 — Surah Ash-Shuara 26:162

Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce

Verse 163 — Surah Ash-Shuara 26:163

Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 164 — Surah Ash-Shuara 26:164

Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu

Verse 165 — Surah Ash-Shuara 26:165

Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai

Verse 166 — Surah Ash-Shuara 26:166

Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa

Verse 167 — Surah Ash-Shuara 26:167

Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)

Verse 168 — Surah Ash-Shuara 26:168

Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa

Verse 169 — Surah Ash-Shuara 26:169

Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa

Verse 170 — Surah Ash-Shuara 26:170

Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya

Verse 171 — Surah Ash-Shuara 26:171

Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa

Verse 172 — Surah Ash-Shuara 26:172

Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu

Verse 173 — Surah Ash-Shuara 26:173

Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana

Verse 174 — Surah Ash-Shuara 26:174

Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba

Verse 175 — Surah Ash-Shuara 26:175

Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai

Verse 176 — Surah Ash-Shuara 26:176

Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni

Verse 177 — Surah Ash-Shuara 26:177

A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba

Verse 178 — Surah Ash-Shuara 26:178

Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce

Verse 179 — Surah Ash-Shuara 26:179

Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã

Verse 180 — Surah Ash-Shuara 26:180

Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu

Verse 181 — Surah Ash-Shuara 26:181

Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)

Verse 182 — Surah Ash-Shuara 26:182

Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce

Verse 183 — Surah Ash-Shuara 26:183

Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna

Verse 184 — Surah Ash-Shuara 26:184

Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko

Verse 185 — Surah Ash-Shuara 26:185

Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne

Verse 186 — Surah Ash-Shuara 26:186

Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata

Verse 187 — Surah Ash-Shuara 26:187

To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya

Verse 188 — Surah Ash-Shuara 26:188

Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa

Verse 189 — Surah Ash-Shuara 26:189

Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije* ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma

Verse 190 — Surah Ash-Shuara 26:190

Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba

Verse 191 — Surah Ash-Shuara 26:191

Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai

Verse 192 — Surah Ash-Shuara 26:192

Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne

Verse 193 — Surah Ash-Shuara 26:193

Rũhi* amintacce ne ya sauka da shi

Verse 194 — Surah Ash-Shuara 26:194

A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi

Verse 195 — Surah Ash-Shuara 26:195

Da harshe na Larabci mai bayãni

Verse 196 — Surah Ash-Shuara 26:196

Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko

Verse 197 — Surah Ash-Shuara 26:197

Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi

Verse 198 — Surah Ash-Shuara 26:198

Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa

Verse 199 — Surah Ash-Shuara 26:199

Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba

Verse 200 — Surah Ash-Shuara 26:200

Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi

Verse 201 — Surah Ash-Shuara 26:201

Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi

Verse 202 — Surah Ash-Shuara 26:202

Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba

Verse 203 — Surah Ash-Shuara 26:203

Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne

Verse 204 — Surah Ash-Shuara 26:204

Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa

Verse 205 — Surah Ash-Shuara 26:205

Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru

Verse 206 — Surah Ash-Shuara 26:206

Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu

Verse 207 — Surah Ash-Shuara 26:207

Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare* su

Verse 208 — Surah Ash-Shuara 26:208

Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi

Verse 209 — Surah Ash-Shuara 26:209

Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba

Verse 210 — Surah Ash-Shuara 26:210

Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba

Verse 211 — Surah Ash-Shuara 26:211

Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa

Verse 212 — Surah Ash-Shuara 26:212

Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne

Verse 213 — Surah Ash-Shuara 26:213

Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba

Verse 214 — Surah Ash-Shuara 26:214

Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci

Verse 215 — Surah Ash-Shuara 26:215

Kuma ka sassauta fikãfikanka* ga wanda ya bĩ ka daga mũminai

Verse 216 — Surah Ash-Shuara 26:216

Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa

Verse 217 — Surah Ash-Shuara 26:217

Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai

Verse 218 — Surah Ash-Shuara 26:218

Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye

Verse 219 — Surah Ash-Shuara 26:219

Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada

Verse 220 — Surah Ash-Shuara 26:220

Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani

Verse 221 — Surah Ash-Shuara 26:221

Shin, (kunã so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka

Verse 222 — Surah Ash-Shuara 26:222

Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi

Verse 223 — Surah Ash-Shuara 26:223

Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne

Verse 224 — Surah Ash-Shuara 26:224

Kuma mawãƙa* halakakku ne ke bin su

Verse 225 — Surah Ash-Shuara 26:225

Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba

Verse 226 — Surah Ash-Shuara 26:226

Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa

Verse 227 — Surah Ash-Shuara 26:227

Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa