Back to Languages

Hausa - Chapter 25 - Al-Furqan

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Furqan 25:1

Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta

Verse 2 — Surah Al-Furqan 25:2

wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkin Sa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa

Verse 3 — Surah Al-Furqan 25:3

Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa

Verse 4 — Surah Al-Furqan 25:4

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana

Verse 5 — Surah Al-Furqan 25:5

Kuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma

Verse 6 — Surah Al-Furqan 25:6

Ka ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai

Verse 7 — Surah Al-Furqan 25:7

Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi

Verse 8 — Surah Al-Furqan 25:8

Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce

Verse 9 — Surah Al-Furqan 25:9

Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki

Verse 10 — Surah Al-Furqan 25:10

Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje

Verse 11 — Surah Al-Furqan 25:11

Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a

Verse 12 — Surah Al-Furqan 25:12

Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta

Verse 13 — Surah Al-Furqan 25:13

Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can

Verse 14 — Surah Al-Furqan 25:14

Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa

Verse 15 — Surah Al-Furqan 25:15

Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma

Verse 16 — Surah Al-Furqan 25:16

Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka

Verse 17 — Surah Al-Furqan 25:17

Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya

Verse 18 — Surah Al-Furqan 25:18

suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku

Verse 19 — Surah Al-Furqan 25:19

To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma

Verse 20 — Surah Al-Furqan 25:20

Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani

Verse 21 — Surah Al-Furqan 25:21

Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma

Verse 22 — Surah Al-Furqan 25:22

A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe* mu

Verse 23 — Surah Al-Furqan 25:23

Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya

Verse 24 — Surah Al-Furqan 25:24

Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla

Verse 25 — Surah Al-Furqan 25:25

Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa

Verse 26 — Surah Al-Furqan 25:26

Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani

Verse 27 — Surah Al-Furqan 25:27

Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo

Verse 28 — Surah Al-Furqan 25:28

Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba

Verse 29 — Surah Al-Furqan 25:29

Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum

Verse 30 — Surah Al-Furqan 25:30

Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa

Verse 31 — Surah Al-Furqan 25:31

Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako

Verse 32 — Surah Al-Furqan 25:32

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa

Verse 33 — Surah Al-Furqan 25:33

Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara

Verse 34 — Surah Al-Furqan 25:34

Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya

Verse 35 — Surah Al-Furqan 25:35

Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi

Verse 36 — Surah Al-Furqan 25:36

Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yin Mu." sai Muka darkãke su, darkãkewa

Verse 37 — Surah Al-Furqan 25:37

Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai

Verse 38 — Surah Al-Furqan 25:38

Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa

Verse 39 — Surah Al-Furqan 25:39

Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa

Verse 40 — Surah Al-Furqan 25:40

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma)

Verse 41 — Surah Al-Furqan 25:41

Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo

Verse 42 — Surah Al-Furqan 25:42

Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya

Verse 43 — Surah Al-Furqan 25:43

Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa

Verse 44 — Surah Al-Furqan 25:44

Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida* suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya

Verse 45 — Surah Al-Furqan 25:45

Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta

Verse 46 — Surah Al-Furqan 25:46

Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi

Verse 47 — Surah Al-Furqan 25:47

Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma)

Verse 48 — Surah Al-Furqan 25:48

Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamar Sa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama

Verse 49 — Surah Al-Furqan 25:49

Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta

Verse 50 — Surah Al-Furqan 25:50

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa* shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci

Verse 51 — Surah Al-Furqan 25:51

Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kõwace alƙarya

Verse 52 — Surah Al-Furqan 25:52

Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma

Verse 53 — Surah Al-Furqan 25:53

Kuma shĩ ne Ya gauwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa

Verse 54 — Surah Al-Furqan 25:54

Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi

Verse 55 — Surah Al-Furqan 25:55

Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa

Verse 56 — Surah Al-Furqan 25:56

Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi

Verse 57 — Surah Al-Furqan 25:57

Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa

Verse 58 — Surah Al-Furqan 25:58

kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa

Verse 59 — Surah Al-Furqan 25:59

Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi

Verse 60 — Surah Al-Furqan 25:60

Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana* ta ƙãra musu gudu)

Verse 61 — Surah Al-Furqan 25:61

Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta

Verse 62 — Surah Al-Furqan 25:62

Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde

Verse 63 — Surah Al-Furqan 25:63

Kuma bãyin Mai rahama* su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya)

Verse 64 — Surah Al-Furqan 25:64

Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu

Verse 65 — Surah Al-Furqan 25:65

Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra

Verse 66 — Surah Al-Furqan 25:66

Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni

Verse 67 — Surah Al-Furqan 25:67

Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa

Verse 68 — Surah Al-Furqan 25:68

Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka

Verse 69 — Surah Al-Furqan 25:69

A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce

Verse 70 — Surah Al-Furqan 25:70

Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai

Verse 71 — Surah Al-Furqan 25:71

Kuma wanda ya tũba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah

Verse 72 — Surah Al-Furqan 25:72

Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci

Verse 73 — Surah Al-Furqan 25:73

Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame* da makãfi

Verse 74 — Surah Al-Furqan 25:74

Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya* mu shũgabanni ga mãsu taƙawa

Verse 75 — Surah Al-Furqan 25:75

Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci

Verse 76 — Surah Al-Furqan 25:76

Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni

Verse 77 — Surah Al-Furqan 25:77

Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku* ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci