Back to Languages

Hausa - Chapter 28 - Al-Qasas

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 15 — Surah Al-Qasas 28:15

Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne