Back to Languages

Hausa - Chapter 28 - Al-Qasas

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 50 — Surah Al-Qasas 28:50

To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai