Back to Languages

Hausa - Chapter 35 - Fatir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 11 — Surah Fatir 35:11

Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an nan Ya sanya ku surkin maza da mãtã. Kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma bã zã a rãyar da wanda ake rãyarwa ba, kuma bã zã a rage tsawon ransa ba fãce yanã a cikin Littãfi. Lalle, wancan mai sauki ne ga Allah