Back to Languages

Hausa - Chapter 36 - Ya-Sin

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ya-Sin 36:1

Verse 2 — Surah Ya-Sin 36:2

Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni* Mai hikima

Verse 3 — Surah Ya-Sin 36:3

Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikin Manzanni

Verse 4 — Surah Ya-Sin 36:4

A kan hanya madaidaiciya

Verse 5 — Surah Ya-Sin 36:5

(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai

Verse 6 — Surah Ya-Sin 36:6

Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne

Verse 7 — Surah Ya-Sin 36:7

Lalle, haƙĩƙa, kalma* tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba

Verse 8 — Surah Ya-Sin 36:8

Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne

Verse 9 — Surah Ya-Sin 36:9

Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani

Verse 10 — Surah Ya-Sin 36:10

Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba

Verse 11 — Surah Ya-Sin 36:11

Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci

Verse 12 — Surah Ya-Sin 36:12

Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani

Verse 13 — Surah Ya-Sin 36:13

Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni* suka jẽ mata

Verse 14 — Surah Ya-Sin 36:14

A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku

Verse 15 — Surah Ya-Sin 36:15

Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi

Verse 16 — Surah Ya-Sin 36:16

Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku

Verse 17 — Surah Ya-Sin 36:17

Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne

Verse 18 — Surah Ya-Sin 36:18

Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku

Verse 19 — Surah Ya-Sin 36:19

Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi

Verse 20 — Surah Ya-Sin 36:20

Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan

Verse 21 — Surah Ya-Sin 36:21

Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne

Verse 22 — Surah Ya-Sin 36:22

Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku

Verse 23 — Surah Ya-Sin 36:23

Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã

Verse 24 — Surah Ya-Sin 36:24

Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna

Verse 25 — Surah Ya-Sin 36:25

Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni

Verse 26 — Surah Ya-Sin 36:26

Aka ce *(masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani

Verse 27 — Surah Ya-Sin 36:27

Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama

Verse 28 — Surah Ya-Sin 36:28

Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama* a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba

Verse 29 — Surah Ya-Sin 36:29

Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu

Verse 30 — Surah Ya-Sin 36:30

Yã nadãma a kan bãyĩ Na! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili

Verse 31 — Surah Ya-Sin 36:31

Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba

Verse 32 — Surah Ya-Sin 36:32

Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurin Mu

Verse 33 — Surah Ya-Sin 36:33

Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci

Verse 34 — Surah Ya-Sin 36:34

Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta

Verse 35 — Surah Ya-Sin 36:35

Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba

Verse 36 — Surah Ya-Sin 36:36

Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba

Verse 37 — Surah Ya-Sin 36:37

Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu

Verse 38 — Surah Ya-Sin 36:38

Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani

Verse 39 — Surah Ya-Sin 36:39

Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa

Verse 40 — Surah Ya-Sin 36:40

Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo

Verse 41 — Surah Ya-Sin 36:41

Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi

Verse 42 — Surah Ya-Sin 36:42

Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa

Verse 43 — Surah Ya-Sin 36:43

Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba

Verse 44 — Surah Ya-Sin 36:44

Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci

Verse 45 — Surah Ya-Sin 36:45

Kuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku

Verse 46 — Surah Ya-Sin 36:46

Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta

Verse 47 — Surah Ya-Sin 36:47

Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya

Verse 48 — Surah Ya-Sin 36:48

Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya

Verse 49 — Surah Ya-Sin 36:49

Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma

Verse 50 — Surah Ya-Sin 36:50

Bã zã su iya yin wasiyya* ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba

Verse 51 — Surah Ya-Sin 36:51

Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu

Verse 52 — Surah Ya-Sin 36:52

Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya

Verse 53 — Surah Ya-Sin 36:53

Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu

Verse 54 — Surah Ya-Sin 36:54

To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 55 — Surah Ya-Sin 36:55

Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi

Verse 56 — Surah Ya-Sin 36:56

Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira

Verse 57 — Surah Ya-Sin 36:57

Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo

Verse 58 — Surah Ya-Sin 36:58

Aminci," da magana,* daga Ubangiji Mai jin ƙai

Verse 59 — Surah Ya-Sin 36:59

Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi

Verse 60 — Surah Ya-Sin 36:60

Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne

Verse 61 — Surah Ya-Sin 36:61

Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya

Verse 62 — Surah Ya-Sin 36:62

Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba

Verse 63 — Surah Ya-Sin 36:63

Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita

Verse 64 — Surah Ya-Sin 36:64

Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci

Verse 65 — Surah Ya-Sin 36:65

A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa

Verse 66 — Surah Ya-Sin 36:66

Dã Mun so, dã Mun shãfe gani *daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani

Verse 67 — Surah Ya-Sin 36:67

Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba

Verse 68 — Surah Ya-Sin 36:68

Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta

Verse 69 — Surah Ya-Sin 36:69

Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne

Verse 70 — Surah Ya-Sin 36:70

Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai

Verse 71 — Surah Ya-Sin 36:71

Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su

Verse 72 — Surah Ya-Sin 36:72

Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci

Verse 73 — Surah Ya-Sin 36:73

Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba

Verse 74 — Surah Ya-Sin 36:74

Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su

Verse 75 — Surah Ya-Sin 36:75

Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã)

Verse 76 — Surah Ya-Sin 36:76

Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa

Verse 77 — Surah Ya-Sin 36:77

Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar

Verse 78 — Surah Ya-Sin 36:78

Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu

Verse 79 — Surah Ya-Sin 36:79

Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne

Verse 80 — Surah Ya-Sin 36:80

Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi

Verse 81 — Surah Ya-Sin 36:81

Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi

Verse 82 — Surah Ya-Sin 36:82

UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi)

Verse 83 — Surah Ya-Sin 36:83

Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku